News
Mutane 5 ne suka mutu a hatsarin mota A Enugu
Mutane 5 ne suka mutu a wani hatsarin mota da ya afku a hanyar Enugu zuwa Awka zuwa Onitsha a ranar Alhamis.
Kwamandan hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) a jihar Enugu, Joseph Toby, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) a Enugu cewa mutane 15 – maza 10 da mata 5 – sun samu munanan raunuka a hadarin.
Taliban ta kama wani da ake zargin ya yi uwa da ‘yarta fyaɗe
Ya ce, motoci biyu da hadarin ya rutsa da su sun yi karo da juna ne a yayin da suke amfani da layi daya.
“Mutane 20 ne a cikin motocin kasuwanci guda biyu; biyar da suka mutu uku maza ne mata biyu a cikin motar,” inji shi.
Ya kara da cewa an kai wadanda suka jikkata zuwa asibitin kashi na kasa da ke Enugu da kuma wani asibiti mai zaman kansa dake kan titin Enugu-Awka-Onitsha.
Mista Toby ya ce an ajiye gawarwakin wadanda suka mutu a dakin ajiye gawa na Asibitin Colliery da ke Enugu.
Ya daura laifin hatsarin a kan rashin da’a, da saurin gudu da kuma birki.
Sai dai shaidun gani da ido, sun dora laifin hatsarin kan rashin kyawun titi wanda ya tilastawa masu ababen hawa yin tuki a kan cunkoson ababen hawa a maimakon yin amfani da titin da babur.
