Connect with us

News

An Fuskanci Wani Yanayin Zafi Na Tarihi Ranar Talata A Kasashen Duniya

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Advertisement

An fuskanci wani yanayin zafi da ba a taba samun irin sa ba cikin shekaru a kasashen duniya a ranar Talata wanda ranar Laraba na iya zama rana ta uku a jere da za a yi fama da wannan zafi da ya kafa tarihi a duniya.

Hakan shine na baya-bayan nan a cikin jerin matsanancin canjin yanayi wanda ke da tsoratarwa, sai dai yanayin bai ba masana kimiyya mamaki ba.

Advertisement

Gwamnan Taraba Ya Rage Wa Daliban Jami’a Rabin Kudin Makaranta

Ranar matsanancin zafi a duniya
Ranar matsanancin zafi a duniya
Matsanancin zafin na duniya ya kai maki 62.9 na Fahrenheit (digiri 17.18 Celsius) a ranar Talata, bisa ga binciken cibiyar nazarin yanayi ta Jami’ar Maine. A ranar Litinin, matsanancin zafin ya kai maki 62.6 na Fahrenheit (digiri 17.01 Celsius), wanda ya kafa tarihin da ya dauki tsawon sa’oi 24 kacal.

Wannan irin zafi mai tarihi wata shaida ce ga wadanda dama ke cewa dumamar yanayi na kara tura mu cikin makoma mai zafi, “in ji masanin kimiyyar yanayi na Jami’ar Stanford Chris Field, wanda ba ya cikin masu lissafin.

Advertisement

A ranar Laraba, Amurkawa miliyan 38 ne suka tsunduma cikin wani nau’in zafi da aka yi shekarsa, in ji babban jami’ar kimiya Sarah Kapnick.

Ta ce zafi a duniya ya samo asali ne daga dumamar yanayi na El Nino ta tekun Pasifik wanda ke kara zafi a duniya yayin da yake sauya yanayin na duniya, banda sauyin yanayi da mutane ke haddasawa ta wajen girki da itace, da amfani da mai da kuma iskar gas.

Advertisement

-AP

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending