Sports
Dan majalisar Ghana ya nemi afuwar Harry Maguire kan zolayar da ya yi masa a bara
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Wani dan majalisar dokoki na bangaren adawa a Ghana ya nemi afuwar Harry Maguire dan wasan baya na Manchester United, saboda kwatanta kwazonsa da rashin iya gudanarwar gwamnati a fannin tattalin arzikin kasar.
Ghana dai na fama da matsalar hauhawar farashin da ya zarce kashi 35% da kuma taruwar bashi.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya garzaya Gaban kotun koli domin kalubalantar tsige shi
Da yake neman afuwar, Isaac Adongo ya ce dan kwallon baya na Manchester United, Harry Maguire ya canza, har ma ya zama muhimmin dan wasa ga kungiyarsa.
Dan majalisar na Ghana a bara ya yi zolaya da Maguire wanda ya ce ya zame wa Manchester alakakai da ke taimaka wa abokan hamayya ta hanyar cin kansu da kansu.
Bayaninsa ya sanya majalisar dokokin barkewa da dariya, lokacin da ya ce Ghana tana da abin da ya kira Maguire a bangaren tattalin arziki, yayin da yake zargin mataimakin shugaban kasa, Mahamudu Bawumia kan hauhawar farashi da dumbin bashin da ya taru a kan kasar.
Bbc ta ruwaito cewa Gwamnatin Ghana dai na fatan cewa kamar dan kwallon Manchester United, tattalin arzikin kasar ma zai sake farfadowa sanadin wani bashin ceto kasar da tattaunawar da Ghana ke yi don sake lissafin bashin da ke kanta.
