News
Kungiyar Hezbollah da Isra’ila sun yi musayar wuta yayin da ake fuskantar tashin hankali a kan iyaka
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Kungiyar Hizbullah ta Lebanon da Isra’ila sun yi musayar wuta a daidai lokacin da ake ci gaba da samun tashin hankali a kan iyakar Lebanon da Isra’ila.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, Hezbollah ta ce ta kai hari kan wata na’urar radar a kudancin Lebanon da “makaman da suka dace”, wanda kuma ya samu inda ake so “kai tsaye.”
Rusau A Filin Idi : Kotu Ta Bada Umarni A Rufe Asusun Gwamatin jahar Kano Guda 20 A Najeriya
A nata bangaren, rundunar sojin Isra’ila ta ce ta kai hare-hare a wurare da dama a kudancin kasar Lebanon, a matsayin martani ga hare-haren da kungiyar Hizbullah ta kai kan wuraren sojin Isra’ila.
Trt Afirka ta ruwaito cewa a ce ta gano wasu makamai masu linzami da aka harba daga Lebanon zuwa wani sansanin soji da ke kusa da kauyen Arab al Aramshe da ke yammacin Galili da kuma wani shingen tsaro a yankin Hermon.
A wani labarin kuma Rusau A Filin Idi : Kotu Ta Bada Umarni A Rufe Asusun Gwamatin jahar Kano Guda 20 A Najeriya
Ma’aikatar Lafiya da ke Gaza ta tabbatar da cewa an kai gawawwakin mutum 73 da kuma mutum 123 wadanda suka samu rauni asibitin Al-Aqsa a sa’o’i 24 da suka gabata.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare a fadin Falasdinu ba kakkautawa.
Kasashen duniya da dama na ci gaba da Allah wadai da kan kisan da Isra’ila ke yi a Gaza.
