News
Rusau A Filin Idi : Kotu Ta Bada Umarni A Rufe Asusun Gwamatin jahar Kano Guda 20 A Najeriya
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta bayar umarnin rufe asusun gwamatin jihar Kano a wasu bankunan kasuwanci guda 20 a Najeriya.
Mai shari’a I.E Ekwo ya bayar da wannan umarni ne a wata kara ta Incorporated Trustees Incorporated ta masu shagunan filin masallacin Sallacin Idi da kungiyar ‘yan kasuwa suka shigar akan rushi madu shagunansu wanda suka bayyana a matsayin haramtaccen matakin da gwamatin jihar ta dauka a watan Yunin 2023.
Muddun Isra’ila ta ce za ta kutsa Turkiyya kashe ‘Yan Hamas, za ta ‘Yaba Wa Aya Zaki’ – Erdoğan
SOLACEBASE ta ruwaito wadanda suka shigar da karar kamar haka Alhaji Awalu sai’du, Ifeanyi Nwobodo, Alhaji Sani Uba, Alhaji Abdullahi A. Idris, da wasu mutane 25 sun kai karar karar gwamatin jihar Kano, a cikin masu bin bashi, har naira milliyan dubu 30 .
Umarnin yana kunshe ne a cikin daftarin hukuncin da aka bayar a ranar 28 ga Nuwamba, 2023 kuma aka bai wa manema labarai ranar Larabar nan.
Details soon..
