Connect with us

News

Muddun Isra’ila ta ce za ta kutsa Turkiyya kashe ‘Yan Hamas, za ta ‘Yaba Wa Aya Zaki’ – Erdoğan

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

 

Advertisement

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya gargadi mahukuntan Isra’ila da kada su bi ‘yan kungiyar Hamas a yankin Turkiyya.

“Idan suka kuskura su dauki irin wannan matakin kan Turkiyya, to za su dandana kudar su ta yadda ba za su iya farfadowa ba har abada,” in ji Erdoğan a lokacin da ya dawo daga Qatar a ranar Laraba.

Advertisement

Bayan Hutun Wata 7 Kotu ta sake dage sauraron Shari’ar Kisan Ummita zuwa 2024

Bayanin na Erdoğan ya fito ne daga ofishin sadarwarsa da ke amsa tambaya kan shirin hukumar leken asirin kasar Isra’ila na kashe ‘yan kungiyar Hamas a kasashen waje.

Tun da farko a ranar Litinin, kamfanin dillancin labarai na Anadolu ya ambato hukumomin leken asirin Turkiyya na cewa Isra’ila za ta fuskanci “mummunan sakamako” idan ta kai hari kan ‘yan Hamas a Turkiyya.

Advertisement

Jaridar Wall Street Journal a baya ta bayar da rahoton cewa ma’aikatan sirri na Isra’ila suna shirin bin kasashen da domin kashe shugabannin Hamas a duniya bayan kawo karshen yakin Gaza.

Premium Times ta ruwaito cewa Turkiyya na da alaka da kungiyar Hamas mai kishin Islama ta Falasdinu, ta kuma yi watsi da sanya kungiyar a matsayin ‘yan ta’adda, wanda kasashen Turai da Amurka ke yi.

Advertisement

A wani labarin kuma Bayan Hutun Wata 7 Kotu ta sake dage sauraron Shari’ar Kisan Ummita zuwa 2024

Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.

Advertisement

Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.

A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.

Advertisement

Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending