News
Bayan Hutun Wata 7 Kotu ta sake dage sauraron Shari’ar Kisan Ummita zuwa 2024
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Bayan wata bakwai babu zaman kotu, an sake dage sauraron shari’ar dan Chinan da ake zargi da kisan budurwarsa Ummulkusum Buhari (Ummita) a Kano zuwa shekarar 2024.
A yau ne aka ci gaba da sauraren shari’ar dan kasar Chinan Mista Frank Quangrang Geng, wanda gwamnatin Kano ta gurfanar bisa zarginsa da kisan budurwarsa Ummita a jihar.
Bukola Saraki Yace Kisan Masu Mauludi A Jihar Kaduna Abun Takaici Ne
Shari’ar da da ake yi tsakanin Gwamnatin Jihar da ke dan kasar Chinan ne bayan shafe watanni bakwai ba tare da zaman shari’ar ba, saboda shari’o’in zabe.
Aminiya ta ruwaito cewa A zaman, Lauyan Dan China Barista Muhammad Danazumi ya nemi afuwar kotun bisa rashin kawo rubutaccen bayanansa na karshe daga bangarensu, sakamakon ayyukan shari’oin zabe da suka dauke masa hankali.
“A yanzu haka na kusa kammala rubuta bayanaina na karshe, zuwa makon gobe zan kammala sannan in mika wa bangaren masu kara,” kamar yadda ya shaida wa kotu.
Sai dai lauyan gwamnati, Barista Aisha Mahmud, ta yi suka game da wannan bayani na bangaren wadanda ake kara.
Amma ta ce babu yadda za su yi, “Yanzu dole sai mun jira sun kammala rubuta bayanansu na karshe sannan mu kuma mu bayar da amsa. Daga karshe kuma sai a yanke hukunci,” in ji ta.
Ta kuma nemi kotu da ta ja hankalin lauyan wanda ake kara da su mayar da hankali kan shari’ar duba da yanayin kes din wanda ya shafi kisan kai.
Alkalin kotun, Mai Shari’a, Sanusi Ado Ma’aji, ya dage shari’ar zuwa ranar 8 ga watan Janairu 2024.
A wani labarin kuma Bukola Saraki Yace Kisan Masu Mauludi A Jihar Kaduna Abun Takaici Ne
Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.
Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.
A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.
Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.
