News
Hukumar NDLEA Ta Tarwatsa Wasu Kungiyoyin Ta’ammuli Da Hodar Iblis A Abuja Da Kano
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, ta sanar da cewa ta samu nasarar tarwatsa wasu dillalan safara da sayar da miyagun kwayoyi da ke aiki a jihohin Kano da Abuja.
Leadership ta ruwaito cewa Kakakin hukumar NDLEA, Femi Babafemi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, inda ya ce, an samu nasarar tarwatsa wata kungiyar masu safarar hodar iblis da tabar heroin tare da kama Onyeka Uba mai shekaru 42 a unguwar Sabon Gari a jihar Kano.
Dangote ya kaddamar da tallafin rabon abinci na Naira Biliyan 15
Babafemi ya bayyana cewa, an kwato kilo 1.805 na haramtattun abubuwa daga hannun wanda ake zargin a ranar Litinin 18 ga watan Maris.
An kuma kama wani wanda ake zargi mai suna Ubale Sani mai shekaru 49 da tabar wiwi mai nauyin kilo 51.5 a unguwar Chiromawa da ke Kano.
Hakazalika, jami’an rundunar ta NDLEA, sun kuma dakile ayyukan wata kungiyar ta’ammali da hodar Iblis a Abuja a karshen mako tare da kama wasu shugabannin kungiyar guda uku.
