Connect with us

News

JAMB Ta Saki Sakamakon Jarrabawar UTME  Na  Shekarar 2024.

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Hukumar JAMB mai shirya jarrabawar neman shiga manyan makarantun gaba da sakandire a Najeriya, ta sanar da sakin sakamakon jarrabawar da dalibai suka zana a bana.

Advertisement

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Dr Fabian Benjamin ya fitar ranar Lahadi a Abuja, babban birnin tarayya kamar yanda Jaridar Punch ta ruwaito 

Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa Ya Caccaki Gwamnonin Arewacin Nijeriya Da Suka Yi Tafiya Zuwa Kasar Amurka Taro Kan Tsaro

Hukumar shigar da manyan makarantu ta hadin gwiwa ta kammala shirye-shiryen fitar da sakamakon jarrabawar kammala manyan makarantu na shekarar 2024.

Advertisement

Magatakardar Hukuma  ta JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede, na shirin ganawa da manema labarai a Abuja a yau  Litinin dan fitar da sakamakon da kuma abubuwan da suka danganci hakan, kamar yadda  sanarwa da aka raba wa manema labarai a babban birnin tarayya.

Duk da haka, akwai alamun cewa sakamakon da za a fitar a yau  Litinin ya kasance na dalilai da suka zana  UTME a cikin ‘yan kwanaki na farko, yayin da wasu za a fitar da su bayan an kammala.

Advertisement

Tun da farko dai hukumar ta fayyace cewa an yanke shawarar jinkirta fitar da sakamakon na ‘yan kwanaki ne domin a ba da isasshen lokaci domin yin nazari sosai.

Wannan matakin, a cewar hukumar jarrabawar, an dauki wannan mataki ne domin tabbatar da gaskiya da ingancin sakamakon da aka samu, tare da tabbatar da cewa babu shakka ko rashin tabbas, musamman dangane da batutuwan da suka shafi kwaikwaya, gaurayawan na’urorin zamani, da sauran nau’ukan munanan ayyuka.

Advertisement

A cikin makon da ya gabata, sama da ’

dalibai miliyan 1.9 ne suka yi rajista don jarrabawar 2024 ta UTME a cikin sama da cibiyoyin gwajin Kwamfuta 700 a duk faɗin ƙasar.

Advertisement

A yau ne ake sa ran kammala jarrabawar shekarar 2024, wadda aka fara a ranar Juma’a 19 ga Afrilu, 2024.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending