Connect with us

News

Yau Marigayi Tsohon Shugaban Mulkin Sojin Nigeria Janar Sani Abacha Ke Cika Shekara 26 Da Rasuwa.

Published

on

DAGA YASIR KABIRU MUHAMMAD

A ranar Litinin 8 ga watan Yunin 2023 Marigayi Janar Sani Abacha ya cika shekara 26 da rasuwa.

Advertisement

Janar Sani Abacha shi ne shugaban mulkin sojin Najeriya soji na 7. Ya kuma rasu ne a kan mulki a ranar 8 ga watan Yuni, 1998.

Kudirin kafa sabuwar jiha ga Inyamurai ya wuce karatu na daya a zauren Majalisar Dattijan Nigeria. 

A ranar rasuwarsa ce kuma aka yi masa suttura aka binne shi a jihar Kano inda nan ne mahaifarsa.

Advertisement

 

TARIHIN ABACHA A TAKAICE

Advertisement

An haifi Marigayi Abacha ne a Kano a ranar Litinin 20 ga watan Satumbar 1943.

Dan asalin jihar Borno ne da ya tashi a Kano ya kuma mayar da Kano ta zamo gida a gare shi.

Advertisement

Ya auri mai dakinsa Maryam Abacha ‘yar kabilar Shuwa Arab daga jihar Borno a shekarar 1965 wadda ta haifa masa ‘ya’ya maza 6, mata 3.

Yana kan mulki Maryam Abacha ta haifa masa dan autansa mai suna Mustapha a shekarar 1994.

Advertisement

Rahotanni na nuni da cewa Marigayi Sani Abacha shi ne Shugaban Kasar Najeriya na soji daya tilo da bai taba tsallaken mukamin soji ba har ya zama shugaban kasa mai mukamin Janar.

 

Advertisement

FARFADO DA TATTALIN ARZIKI.

Duk da yadda wasu ke kallon mulkin sojin Marigayi Janar Abacha a matsayin mai tsauri tare da rashin sassauta wa bangaren kafafen yada labarai da fadin albarkacin baki, tsohon shugaban kasar ya kokarta wajen farfado da tattalin arzikin Najeriya.

Advertisement

Ya kuma taka gagarumar rawa wurin alkinta asusun waje na Najeriya daga Dalar Amurka miliyan 494 zuwa biliyan 9 da miliyan 600 a mulkinsa.

Gwamantin Abacha ta kuma biya kaso mafi yawa na bashin da ake bin Najeriya.

Advertisement

Ya kuma dakatar da matakin gwamnatocin baya na sayar da kadarorin gwamnati ga ’yan kasuwa, bisa hujjar cewa ba a gina gwamnati domin cin riba ba, sai domin ’yan kasa su ci gajiyar ta.

Janar Sani Abacha ya rage hauhawar farashin kayan masarufi da kashi 54 bisa 100 domin saukaka wa talakawa radadin rayuwa.

Advertisement

Ya kuma yi nasarar yin haka ne a lokacin da farashin gangar man fetur yake Dalar Amurka 15 a kasuwannin duniya.

 

Advertisement

BABBAN AMBATON A CIKIN GIDA

 

Advertisement

Babban aikin da aka fi ambaton Marigayi Abacha da shi shi ne kafa hukumar PTF.

Hukumar ta rika amfani da wani bangare na kudin da ya karu na litar mai tana gudanar da manyan ayyuka a faɗin kasar.

Advertisement

PTF ta yi fice wurin yin manyan ayyuka da samar da kaya masu matukar nagarta ga bangarori daban-daban a fadin Najeriya.

Ta rika samar da motoci da litattafai da gine gine da sauran kayan karatu kyauta a dukkan matakan ilimi.

Advertisement

Kuma gina manyan titunan da aka dade an cin moriyarsu a dukkan yankunan kasar.

Hukumar ta kuma bayar magunguna da kayan kul da marasa lafiya a asibitoci fadin kasar.

Advertisement

 

KUDADEN ABACHA’

Advertisement

Wani abu da ake ta cece-ku-ce a kai bayan rasuwar Marigayin shi ne zarginsa da boye kudade a kasashen Turai.

Irin wadannan kudaden ne gwamnatocin da suka biyo bayansa ke karbowa a lokaci zuwa lokaci domin aiwatar da wasu ayyukan ci gaban kasa.

Advertisement

Ko a baya-bayan nan ma gwamnatin Tsohon  shugaban kasa Muhammadu Buhari ta karbo irin wannan kudaden.

Wani abu da sunan Marigayi yayi kauri a kai tun bayan mutuwarsa shi ne batun kudin da ake cewa ta tara a kasashen Turai, kuma gwamnatocin da suka biyo sun yi ta kokarin karbo ire iren kudin.

Advertisement

Ko a kwanakin baya ma gwamnatin shugaba Buhari tayi nasarar karbo wani kaso na kudin da ake alaka ta wa da tsohon shugaban kasa Janar Sani Abacha

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending