News
Yanzu-Yanzu: Gwamnatin Kano Ta Saka Ranar Komawa Makarantar Firamare Da Sakandire
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Gwamnatin jihar Kano ta sanar da ranar Lahadi 15 ga watan Satumba a matsayin ranar komawa makaranta ga daliban makarantun kwana na gwamnati da masu zaman kansu a jihar domin fara karatun zangon karatu na 2024/2025.
Yayin da daliban makarantun jeka-ka-ka-dawo a fadin jihar zasu koma makaranta a ranar Litinin, 16 ga watan na Satumba.
Gwamnatin Kano Ta Dakatar Da Tsawaita Wa’adin Ma’aikan Jihar 4,000 Da Ganduje Ya Yi
Idan za a iya tunawa dai, a ranar Asabar 7 ga watan Satumba ne, kwamishinan ilimi, Alhaji Umar Haruna Doguwa ya sanar da dage ranar komawa makarantar.
A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun daraktan yada labarai na ma’aikatar ilimi, Balarabe Abdullahi Kiru, ya bukaci iyaye da su tabbatar da dalibai sun koma makarantun su a ranar.
Sanarwar ta kuma bukaci, dalibai da su kaucewa kawo haramtattun abubuwa zuwa makarantar kamar su wukake da Reza kuma su kasance masu bin doka.
