Connect with us

News

Babbar Motar Dakon Yashi Ta Hadasa Hadarin Da Ya Haifar Da Mutuwar 3, Jikkata 3 A Kano

Published

on

 

Wani direban babbar motar dakon yashi ya haifar da hadari mai tsanani a yayin da ya bijirewa umarnin tsaiwar da danjar ta yi masa a kan titin zuwa Fadar Gwamnatin Jihar Kano. Sakamakon hadarin, mutum daya ya rasu, yayin da wasu matasa uku suka jikkata.

Advertisement

Shaidun ganin da ido sun bayyana cewa, direban ya keta dokar tsayawa da danjar ta yi masa, wanda hakan ya haifar da hatsarin.

Harkokin Yau Da Kullum Sun Tsaya Cik A Wasu Biranen Nijar Sakamakon Rashin Man Fetur 

An dauki matakan gaggawa na kai wa wadanda abin ya shafa asibiti, amma daya daga cikin matasan ya sha wahala sosai har ya rasu.

Advertisement

Jami’an Tsaro sun fara bincike kan lamarin, yayin da aka kira ga direbobi da su rika bin ka’idojin zirga-zirgar ababen hawa domin guje wa irin wannan masifu.

Jaridar INDA RANKA ta ruwaito cewa Kanwa sun yi kuka da irin wannan hadarin da ke faruwa akai-akai, inda suka yi kira ga hukuma da ta daukaka matakan tsaro a kan tituna.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending