News
Wata Mahaifiya Ta Mutu A Wajen Da ‘Yarta Ke Rubuta Jarrabawar JAMB
Wata Mahaifiya mai suna Oluwasola Victoria Adebayo ta rasu a wani yanayi mai tayar da hankali yayin da take jiran ‘yarta da ke rubuta jarrabawar shiga jami’a ta JAMB a Ilara-Mokin Junction, cikin ƙaramar hukumar Ifedore ta jihar Ondo.
Rahotanni sun nuna cewa matar ta raka ‘yarta zuwa cibiyar jarrabawar da safiyar ranar, amma jim kaɗan bayan isarsu, sai ta fara jin jiki ya yi sanyi kafin daga bisani ta faɗi ƙasa kwatsam.
JAMB Ta Saki Sakamakon Ɗalibai Miliyan 1.9
Mutanen da ke wurin sun yi ƙoƙarin kai mata dauki cikin gaggawa, sai dai hakan bai yi nasara ba, inda aka tabbatar da rasuwarta nan take.
A yayin da lamarin ya faru, ‘yarta na cikin ɗakin jarrabawa tana ci gaba da rubuta takardar, ba tare da sanin abin da ke faruwa a waje ba.
Wani shaida ya bayyana cewa marigayiyar, wadda aka fi sani da “Mummy Ayo,” ta bayyana tun da safe cewa za ta raka ‘yarta zuwa jarrabawar, abin da ya ƙara jawo jimami ga jama’ar da suka halarci wurin.
Lamarin ya janyo taruwar jama’a da suka nuna alhini kan wannan mutuwa ta bazata.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sanda a jihar Ondo, DSP Abayomi Jimoh, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa an miƙa gawar marigayiyar ga ɗanta, Apapa Olamilekan, bayan kammala bincike.
