News
Likitocin Jinya da Ungozoma sun janye yajin aiki
Ƙungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta Ƙasa (NANNM) ta janye yajin aikin da ta fara, in ji Ministan Lafiya, Ali Pate
Yayin da ya ke magana da manema labarai bayan wata ganawar sirri a yau Juma’a, Pate ya bayyana cewa an yanke shawarar dakatar da yajin aikin ne bayan an cimma yarjejeniya da shugabancin ƙungiyar.
Sai dai shugabannin ƙungiyar sun ƙi yin magana da manema labarai bayan ganawar ta sirri da aka yi a yau din.
Ƙungiyar ta fara yajin aikin na gargadi ne a ranar 29 ga Yuli, 2025, biyo bayan zargin gwamnatin tarayya da rashin amsa gamsasshiya ga wa’adin kwanaki 15 da suka bayar tun daga ranar 14 ga Yuli, 2025.
Advertisements
