News
Rukunin jami’o’i na MAAUN ta ƙulla yarjejeniyar koyar da Turanci, musayar ɗalibai da Kwalejin Seneca a Canada
Kamfanin rukunin makarantun jami’o’i na MAAUN ta ƙulla wata yarjejeniyar fahimtar juna (MoU) da Kwalejin ilimin darussan fikira da fasaha ta Seneca da ke kasar Canada, domin ba da horaswa kan naƙaltar Turanci da musayar ɗalibai da sauransu.
Rukunin jami’o’in MAAUN sun haɗa da jami’a mai suna Canadian University of Nigeria da ke Abuja; da jami’ar Franco British International University da ke Kaduna; da jami’ar Maryam Abacha American University da ke Maradin ƙasar Nijar; da jami’ar Maryam Abacha American University da ke Kano.
Gamayyar Kungiyoyin ECOWAS Ta Karrama Sanata Barau Jibrin Da Kyautar Girmamawa
Mamallakin jami’o’in Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, ne ya sanya hannu a madadin dukkan jami’o’in 4 a yayin da David Agnew ya sanya hannu a madadin Kwalejin fasaha ta Seneca.
An ƙulla wannan yarjejeniya ce a ranar Alhamis, 4 ga watan Satumba, a matsayin wani ɓangare na nuna himmatuwa ga ƙulla alaƙa tsakanin jami’o’in huɗu da takwarorinsu a faɗin duniya da nufin bunƙasa ƙirƙira da bincike (nazari).
Sakamakon wannan yarjejeniya na nufin MAAUN ta amince ta yi bayar da bayanai da tallafi da kwarewar da take da ita wajen cimma muradan da suke haɗu a kansu.
MAAUN na sa ran ɗaliban jami’o’inta za su samu horaswa a fannin Turanci ta amfani da intanet da damarmaki ga ɗaliban na cigaba da karatunu a can Kwalejin Fahasa ta Seneca.
Sauran bangarorin sun hada da damarmaki ga ma’aikatan MAAUN na samun shawarwari a kan harkokin ilimi daga Seneca da bunƙasa haɗin guiwa ds abin da ya shafi karkatar da tsarin karatu wanda Seneca za ta taimaka wa MAAUN wajen dubawa.
Har’ila yau akwai batun tallafawa ɗaliban MAAUN wajen zuwa Seneca, domin samun damar tallata damarmakin ga ɗaliban Seneca da ke sha’awar samun ilimi a MAAUN da sauransu.
A nasa jawabin, wanda ya assasa makarantar MAAUN, Adamu Abubakar Gwarzo, ya ba da tabbacin mai da hankali daga jami’o’in domin aiwatar da wannan yarjejeniya da nufin bunƙasa bincike da ƙirƙira.
Ya kuma nuna jin daɗinsa kan yadda Seneca da MAAUN suka fahimci juna tare da fatan haɗin guiwar zai zama wata hanya ta kyautata yin aiki tare.
