News
Jami’an ‘Yan Sandan Sun Kama Tsohuwa Mai Shekaru 50 Bisa Zargin Dillancin Kayan Maye A Jigawa
Rundunar ‘Yan Sandan jihar Jigawa ta samu nasarar cafke wata tsohuwa mai suna Fati Bala mai shekaru 50, wacce ake zargin tana jagorantar dillancin miyagun ƙwayoyi a a Unguwar Kwari, garin Gujungu dauke da kwalabe 40 na Madarar Sukudayin.
Binciken farko ya nuna cewa matar tana daga cikin manyan dillalan miyagun ƙwayoyi a yankin.”
Kakakin rundunar, SP Shiisu Lawan Adam, ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya aikewa manema labari, inda ya ce nasarar ta samu ne karkashin jagorancin Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar, CP Dahiru Muhammad.
Haka zalika a wani sumame da jami’an rundunar suka kai a Garuruwan Dutse da Sara, an cafke mutum uku,Sanusi Shamaki, Unguwar Garu, Abubakar Sama’ila, Burtalan, Abubakar Murtala, Unguwar Jata.
An kama su ne da kayan maye da suka hada da, Sinkin ganyen tabar wiwi 69, Kwayar D5 guda 595, Exol 132, Tramadol 61, Sholisho roba 30, Diazepam 8, Lara 17,Kwalaben Sukudayin 40,Zungureriyar wuka guda 1, Kudi naira 8,08
A hannu guda, rundunar ta kama wani Ado Ya’u a kauyen Matafari, karamar hukumar Malam Madori, bisa zargin sata. An karɓo saniya ɗaya daga hannunsa. Ana ci gaba da gudanar da bincike domin gurfanar da dukkan su a gaban kotu.
