News
Kada ki binciki wayar mijinki ba tare da izinsa ba – Gargadin Shehu Sani
Tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani ya gargadi, mata da su kauce wa bincikar wayoyin mazajensu ba tare da izini ba, yana mai cewa yin haka shine zamna lafiyar su.
Sanata Sani ya bayyana haka a shafinsa ta X inda ya kara da cewa ” Idan ba za ka/ki iya jure wa sanin gaskiyar lamari ba to kada ki neme shi.
Jami’an Tsaro Sun Kama Mutane Biyu da Suke Kai wa ‘Yan Bindiga Kayan Masarufi
Ya kara da cewa “Idan Shaidan ya zuga ki ki binciki wayar mijin ki, ki toshe kunnuwar ki, domin so ya ke ya bude miki ido, amma kuma ya yamutsa lamarin ki, zuciyar ki ta yi sallama da zaman lafiya.
Sai dai kuma maganar mai kama da shagube, ya yi daidai da dokar Najeriya inda ya laifantar da duk wanda ya yi wa wani bincike ba tare da izini.
Dokar Najeriya ta ce idan haka ya auku, to hukunci za ta iya hawa kan wanda ya aikata na laifin yin kutse ga abinda ba huruminsa bane.
