News
Yadda Wani Hatsarin Mota Ya Yi Ajalin Mai Babur
Wani hatsarin mota da ya auku a ranar Alhamis ya yi sanadin mutuwar wani mai Babur a kan titin Apapa–Oshodi, kusa da Ibafon, a jihar Legas.
Rahotanni sun ce hatsarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:30 na safe, lokacin da wata mota kirar Honda Accord ta yi karo da wata babban tirela, lamarin da ya haifar da firgici a tsakanin direbobi da masu wucewa a wajen.
Wani shaida mai suna Tunde ya shaida wa manema labarai cewa, “Tirelan tana tafiya da sauri yayin da motar Honda ta ke ƙoƙarin wuce ta. A lokacin, wani mai Babur da ke tahowa daga akasin hanya ya yi karo da motar, wanda hakan ya janyo mutuwarsa nan take.”
Shaidu sun ce direban tirelan ya tsere bayan faruwar lamarin, inda ya bar motarsa da kuma gawar mamacin a wurin.
’Yan sanda daga ofishin yankin sun isa wajen bayan ɗan lokaci, suka killace yankin, sannan suka kama direban motar Honda domin bincike. Haka kuma, an dauke gawar mamacin daga wurin don kai ta asibiti.
Rahotanni sun ce hatsarin ya sake tunzura jama’a game da yadda masu babura ke bin hanyoyi ba bisa ka’ida ba a wasu sassan birnin Legas.
