Connect with us

News

‎An Kama Wani Mutum Kan Zargin Kashe Matarsa Mai Shekaru 15, A Sakkwato ‎

Published

on

Unguwa gawa

Rundunar ’yansandan Jihar Sakkwato ta kama wani mai shekaru 25 a duniya, Sufiyanu Aliyu, daga ƙauyen Gwanyal a ƙaramar hukumar Tangaza, bisa zargin kashe matarsa mai shekaru 15, Suwaiba Abubakar Bawa.

‎’Yansanda sun ce lamarin ya faru ne a ranar 27 ga watan Oktoba, 2025, bayan rikici ya ɓarke tsakanin ma’auratan.

Advertisement

Za Mu Ƙara Ƙaimi Wajen Kai Wa ‘Yan Bindiga Hare-Hare Ta Sama – Hafsan Sojin Sama

‎Kakakin rundunar, DSP Ahmad Rufai, ya bayyana cewa rundunar ta samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 8 na dare, inda jami’ai suka garzaya wajen da abin ya faru.

‎Bincike ya nuna cewa wanda ake zargi ya soki matarsa da wuƙa yayin da suke faɗa.

Advertisement

‎’Yansanda sun samo wuƙar da ake zargin ya yi amfani da ita wajen kisan, sannan suka kai gawar mamaciyar asibiti, inda likita ya tabbatar da mutuwarta.

‎Rufai, ya ce wanda ake zargi ya amsa laifinsa, kuma an gurfanar da shi a kotu, yayin da aka miƙa shi sashen binciken manyan laifuka na jiha (SCID) domin ƙara bincike.

Advertisement

‎Kwamishinan ’yansanda na jihar ya yaba wa jami’ansa bisa yadda suka hanzarta kai ɗauki, tare da tabbatar wa da jama’a cewa za a tabbatar da adalci a cikin lamarin.

 

Advertisement

LEADSHIP HAUSA

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending