Connect with us

Labarai

Kamfanin jirgin saman Azman ya dakatar da zirga-zirga a Kaduna

Published

on

Advertisements
WhatsApp Image 2026 11 04 at 12.03.38 AM

Daga Muhammad Muhammad zahraddin

Kamfanin jrgin saman Azman ya dakatar da zirga-zirga a jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya kwanaki kadan bayan harin da wasu ‘yan bindiga suka kai filin jirgin saman jihar inda suka kashe masu gadi da wasu ma’aikata

Kamfanin ya wallafa a shafinsa na Tuwita cewa zai dakatar da zirga-zirga a Kaduna daga ranar Litinin din da ta wuce.

Kamfanin ya ce ya dauki matakin saboda yanayi na tsaro a filin jirgin saman.

Matakin kamfanin dai ya sa matafiya sun yi cirko-cirko a filin jirgin saman na Kaduna saboda karancin jiragen da za su kai su inda za su je.

Hukumar gudanarwar kamfanin ta sanar da cewa za a dakatar da zirga-zirgar ce zuwa wani lokaci ma’ana kafin yanayin tsaro ya inganta a filin jirgin saman na Kaduna.

Advertisement

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending