News
Gwamnan Kano Zai Gabatar Da Kasafin 2026 Da Ya Haura Naira Tiriliyan Daya Ga Majalisar Dokokin Jihar
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusif, ya bayyana cewa gwamnatinsa ta kammala shirye-shiryen gabatar da kasafin kuɗin jihar na 2026, wanda zai kai naira tiriliyan ɗaya, kasafin kudi da ya kasance mafi girma a tarihin jihar.
Gwamnan ya baiyana hakan ne a yayin taron majalisar Zartarwa na Musamman karo na biyu da aka kira, domin tattaunawa kan kudirin kasafin kuɗin 2026 kafin gabatar da shi a gaban Majalisar Dokokin Jihar Kano a mako mai zuwa.
Najeriya Na Rasa Yara 850,000 Duk Shekara Sakamakon Cututtukan Da Za A Iya Magance Su
Sanarwar da Kakakin gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya aiko wa GTR Hausa a yau Jumu’a ta danganta ƙarin da aka samu a kudirin kasafin kuɗin da gagarumar ƙaruwar da aka samu a kudaden shiga na cikin gida (IGR) da kuma toshe ɓarnar kuɗaɗe a tsarin gwamnati.
