Connect with us

News

K-MAN Ta Taya Christopher Musa Murnar Rantsar da Shi a Matsayin Ministan Tsaro

Published

on

1764874120718

Kano Media Advocacy Network (K-MAN) na mika gaisuwar taya murna ga Janar Christopher Gwabin Musa (Rtd.), tsohon Babban Hafsan Tsaro na Najeriya, bisa nadin da aka yi masa a matsayin Ministan Tsaro na Tarayyar Najeriya, a wannan muƙami da ya dace da kwarewa, jajircewa da tarihin aikinsa na tsawon shekaru a rundunar sojin ƙasar nan.

Ayyukan Janar Musa a rundunar soji sun tabbatar da nagarta, gaskiya, tsantsar shugabanci da cikakkiyar sadaukarwa wajen kare martabar ƙasa da tabbatar da zaman lafiya. Kwarewarsa wajen daidaita harkokin tsaro, haɗa kai tsakanin bangarorin rundunar soji, da aiwatar da muhimman sauye-sauye a sashen tsaro, na kara tabbatar da cewa yana da cikakken hangen nesa da ƙarfin jagoranci da ake bukata a wannan muhimmin lokaci da Najeriya ke ciki.

Advertisement

Daliba Ta Kare Martabar Jami’ar MAAUN Kan Cece-ku-cen Kuɗin Yaye Dalibai

Yayin da ya hau kan wannan sabon muƙami, K-MAN na bayyana cikakken kwarin gwiwa cewa zai yi duk mai yiwuwa wajen fuskantar kalubalen tsaro da suka addabi ƙasa. Yayin da matsaloli irin su ta’addanci, ‘yan bindiga, rikice-rikicen al’umma, da sauran miyagun laifuka ke ƙaruwa, ‘yan Najeriya na fatan zuwan shi zai kawo sabon salo na zaman lafiya, kwanciyar hankali da dorewar tsaro.

 

Advertisement

KIRA

 

Advertisement

K-MAN na roƙon Rt. Hon. Minista Christopher Gwabin Musa da ya:

 

Advertisement

* Yi amfani da gogewarsa mai zurfi da dukkan muhimman hanyoyi da albarkatun da ke hannunsa wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro, musamman a Arewa.

* Mayar da hankali kan matsalolin tsaro da ke tasowa a Jihar Kano, tare da inganta tattara bayanan sirri, hanzarta daukar matakai, da kuma ƙara tallafin gwamnatin tarayya ga hukumomin tsaron jiha.

Advertisement

* Karfafa haɗin kai da tattaunawa mai inganci da Gwamnatin Jihar Kano, domin haɗin gwiwa tsakanin jiha da tarayya shi ne ginshiƙin magance laifuka da kare rayukan al’umma.

* Mayar da hankali wajen samar da sabon tsarin tsaro na zamani wanda ya ta’allaka kan jama’a, wanda zai ƙarfafa amincewa da haɗin kan al’umma a harkokin tsaro.

Advertisement

K-MAN na mara bayan duk wani yunƙuri da zai inganta tsaro, kuma ta yi imani cewa shugabancin Janar Musa zai taka muhimmiyar rawa wajen dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Najeriya.

Muna sake taya Rt. Hon. Minista Christopher Gwabin Musa (Rtd.) murna, tare da yi masa fatan nasara mai ɗorewa a wannan babban aiki na hidimar ƙasa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending