Connect with us

News

Bakin Haure Fiye Da 3,000 Suka Mutu A Yunkurin Shiga Turai A Shekarar 2025

Published

on

1767068580892 1

Fiye da bakin haure 3,000 suka hakala a kokarin shiga kasar Spain a wannan shekara ta 2025 da ke karewa.

Wani rahoton kungiyar kula da ‘yan gudun hijira ta Spain, ta fitar a wannan Litinin ya nunar da cewa alkaluman sun ragu daga na shekarar da ta gabata ta 2024. Fiye da bakin hauren 10,000 suka mutu ko kuma suka bace a shekara ta 2024 a kokarin shiga kasar ta Spain.

Advertisement

Dakarun Soji Sun Hallaka Ƴan Ta’adda Sama Da 80, Sun Ceto Mutane 34

Bakin haure da suka halaka masu neman shiga kasar ta Spain sun fito ne daga nahiyar Afirka, galibi daga kasashen Aljeriya da Somaliya da Sudan da Sudan ta Kudu.

Sannan ma’aikatar kula da harkokin cikin gida ta Spain ta bayyana cewa fiye da bakin haure 35,000 suka shida kasar daga farkon shekarar da muke ciki ta 2025, zuwa wannan wata na Disamba, abin da ke nuna raguwa da kaso 40 cikin 100 na wadanda suka shiga kasar, idan aka kwakwanta ta shekarar da ta gabata ta 2024.

Advertisement

 

DW

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending