Labarai
Ya kamata a bar ‘yan Najeriya su rike makamai domin kare kansu, Jigo a majalisar wakilai

Shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai, Ado Doguwa, ya ce ya kamata a bar ‘yan Najeriya su rike makamai domin kare kansu duba da tabarbarewar tsaro a kasar nan.
Dan majalisar wakiltar mazabar Doguwa/Tudun Wada ta Kano ya bayyana haka ne a zaman da majalisar ta yi a jiya Alhamis a lokacin da ake muhawara kan harin da ‘yan ta’adda suka kai kan wani jirgin kasan fasinja a garin Birnin Gwari na jihar Kaduna.
Doguwa, wanda wannan mummunan al’amari ya kai shi zub da hawaye, yana kan ra’ayin cewa jami’an tsaro sun gaza, don haka bai kamata ‘yan kasa su ci gaba da zama cikin cutarwar ‘yan ta’adda ko ‘yan fashi ba.
A labari makamancin wannan, tsohon dan majalisar dokokin kasar wanda ya wakilci yankin Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa, Sanata Shehu Sani, ya magantu a kan lamarin rashin tsaro.
Shehu Sani ya ce duba ga yadda lamarin tsaro ke kara tabarbarewa a kasar nan, ya kamata a bari yan Najeriya su dunga daukar makamai domin kare kansu a hukumance.
Da yake martani kan hare-haren baya-bayan nan a shafinsa na Twitter a ranar Alhamis, 31 ga watan Maris, Sani ya bayyana cewa tunda gwamnati ta gaza gurgunta ayyukan yan bindiga, cewa ya kamata a bari mutane su kare kansu da kansu.
Sani ya rubuta: “Idan gwamnati da hukumomin tsaro ba za su iya murkushe wadannan yan ta’adda da yan fashi da ke garkuwa da kashe mutanenmu a arewa da kudancin Kaduna ba, ya kamata a baiwa mutane damar daukar makamai a hukumance sannan mu zuba ido mu ga wa ke da kasar.”
-
Labarai7 days ago
Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Yi Wa Masu Digirin Ƙasashen Waje Jarrabawa
-
Labarai3 days ago
Jami’an Tsaro A Pakistan Sun Kama ’Yan Najeriya 20 Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi
-
Labarai2 days ago
Hare-haren Ta’addanci Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutum 835 A Najeriya Cikin Wata Guda – Rahoto
