Connect with us

News

Akalla Shaguna 25 Da Katina 19 Ne Suka Kone Kasuwar Singa Da Ke Kano

Published

on

FB IMG 1770006317582

Akalla shaguna 25 da Katina 19 ne a ka tabbatar sun kone a babbar Kasuwar Singa da ke a birnin Kano.

Mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta jihar Kano Saminu Abdullahi ne ya tabbatar da haka a wata rubutacciyar sanarwa.

Dalilan Da Ya Sa Gwamna Abba Ya Kamata Ya Zabi Murtala Sule Garo A Matsayin Mataimakin Sa

Hukumomi a Kano dai sun bayyana cewar gobarar da haddasa hasarar kaya da su ka kai na miliyoyin Naira kamin daga bisani a ka samu nasarar kashe Wutar.

Wutar ta tashi ne da misalin karfe 5 na Asubah kuma daga nan ne mutane su ka nemi agajin gaggawa daga hukumar kashe gobara ta jihar abin da ya takaita matsalar da kuma kare akalla shaguna 24 daga konewa.

Matsalolin hanya da ke da nasaba da manyanyan Motocin dakon kaya da ake ajiyewa a wurin cikin kasuwar na daga cikin matsalolin da su ka ta’azzara matsalar.

Advertisement

Wutar ta samo asali ne daga wayoyin Wutar lantarki a daya daga cikin shagunan da su ka kone, saidai ba a samu rasa rayka ba.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending