News
Motar Kai Saƙon Kamfanin Amazon Ta Makale A Teku Bayan Direbanta Ya Yi Amfani Da ‘GPS Map’
Wata motar kai saƙo ta kamfanin Amazon ta tsinci kanta a cikin mawuyacin hali bayan da direbanta ya bi umarnin manhajar taswira (GPS), lamarin da ya kai ta har cikin wani yankin gaɓar teku.
Jami’an HM Coastguard Southend sun samu kiran gaggawa a safiyar Lahadi bayan da motar ta maƙale a wurin da ba a saba ganin ababen hawa ba, inda ta kwana a wurin kafin a kai mata dauki.
EFCC ta tsare El-Rufai, a yayin da kotu da ICPC ke jiran zuwansa
Rahotanni sun nuna cewa motar ta shiga wani tsohon hanya mai suna The Broomway da ke a gaɓar tekun Ingila — wata hanya mai tarihin kusan shekaru 600 da ba a gina domin zirga-zirgar motoci ba.
Jami’an tsaron gabar teku sun bayyana cewa wannan hanya tana ratsa yankin laka mai zurfi da kuma wuraren da ruwa kan mamaye lokaci zuwa lokaci, lamarin da ya sa ababen hawa ke fuskantar barazana idan suka bi ta.
Sun ƙara da cewa The Broomway hanya ce mai tsawon kusan mil shida, kuma tana da haɗari matuƙa saboda saurin shigowar ruwa da kuma tabon laka da ke iya jawo nutsewar abin hawa cikin sauƙi.
Hukumomi sun gargadi direbobi da su riƙa tabbatar da sahihancin hanyoyin da suke bi ta manhajojin taswira, musamman a yankunan da ba a saba zirga-zirga ba, domin kauce wa irin wannan haɗari.
