Connect with us

News

Gobarar Singa Ta Sanya Fargabar Tashin Kayan Masarufi A Ramadan

Published

on

WhatsApp Image 2026 02 15 at 13.30.37 768x385
Mummunar gobarar singa ta ƙone tarin shaguna da haddasa asarar dukiya ta biliyoyi.
Advertisements
ads

A wani yanayi da aka faro azumin watan Ramadana, al’ummar jihar Kano da sauran jihohin da suka dogara da kasuwar Singa wajen samun kayayyakin masarufi kama daga ƙananun ƴan kasuwa da kuma ɗaiɗaikun mutane sun shiga tsaka mai wuya, sakamakon ƙarancin kayakin da ake fuskanta dama fargabar hauhawar farashinsu a irin wannan lokaci na buƙata.

Galibi a watan Ramadana al’umma kan buƙaci kayakin masarufi fiye da ko yaushe wanda kuma suna daga cikin kayakin da gobarar ta Singa ta ɓarnata, lamarin da ya sanya ɗimbin magidanta cikin fargaba, sai dai Malam Ɗan Ladi Inuwa ya kore batun tsawwala farashi yana mai sa ran ƴan kasuwar su hankalta wajen sauƙaƙawa jama’a.

Su da kansu ƙananun ƴan kasuwa ko kuma masu shaguna na unguwanni irin Malam Habu, na cike da fargabar ƙarewar kayakin masarufin da ke hannunsu, a wani yanayi da ake ganin ƙarancinsu a kasuwar sakamakon mummunar ɓarnar da wannan gobara ta yi.

To da ya ke tuni ɓangarori da dama ciki har da gwamnatin Najeriya suka sanar da ƙunshin tallafi ga ƴan kasuwar ta Singa a Kano da ya kai naira biliyan 8, fargabar a yanzu bai wuce yadda kason wannan kuɗi zai gudana tsakanin ƴan kasuwar ba, don ganin sun isa ga kowa, kodayake Abdurrahman Abubakar mai baiwa Gwamnan Kano shawara kan harkokin kasuwanni ya bayyana cewa suna da tsari mai kyau wajen rabon.

An dai yi ittifaƙin wannan gobara ta singa ta haddasa ɓarnar da ta haura naira biliyan 30.

 

Advertisement

 

RFI

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending