Connect with us

News

Gwamnatin Aljeriya ta yi wa fursunoni 1,000 afuwa albarkacin watan Ramadan

Published

on

Daga kabiru basiru fulatan

 

Shugaban Aljeriya Abdelmadjid Tebboune ya yi wa fursunoni fiye da 1,000 afuwa domin watan azumin Ramadan.

Advertisement

Wata sanarwa da aka fitar daga ofishinsa ta ce gwamnati za ta yi afuwa ga wasu masu zanga-zanga 70 wadanda mambobin kungiyar Hirak mai fafutukar kafa dimokuraɗiyya ne.

Cikin wadanda aka saki akwai Zaki Hannache wanda aka kama a watan Fabrairu saboda tuhumar da aka yi masa cewa yana yada labaran kanzon kurege baya ga tunzura mutane su aikata laifukan ta’addanci.

Advertisement

Kungiyar Hirak ta fara zanga-zanga ne amanyan biranen kasar ta Aljeriya tun farkon 2019, matakin da ya tilasta wa tsohon shigabna kasar Abdelaziz Bouteflika sauka daga mukaminsa bayan wasu watanni.

Hirak ta ci gaba da zanga-zanga bayan da Tebboune ya zama shugaban kasa, sai dai ya yi watsi da matakin kungiyar da ke tuhumarsa da bin sahun tsohuwar gwamnatin kasar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending