News
An Ceto Daliban Da Aka Sace A Hanyar Zuwa Jarrabawar JAMB
Jami’an tsaro a Jihar Benue sun sanar da ceto wasu dalibai da aka sace yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa rubuta jarabawar Joint Admissions and Matriculation Board (JAMB), tare da wasu fasinjoji, bayan wani samame na hadin gwiwa.
Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Ifeanyi Emenari, ya bayyana hakan a ranar Lahadi, lokacin da yake gabatar da mutum 15 daga cikin waɗanda aka ceto ga gwamnan jihar, Hyacinth Alia, a fadar gwamnati da ke Makurdi.
An Ceto Daliban Da Aka Sace A Hanyar Zuwa Jarrabawar JAMB
A cewar jami’in, an samu nasarar ceton mutanen ne bayan tattara sahihan bayanan sirri da suka kai ga kai samame a maboyar masu garkuwa da mutane. Ya tabbatar da cewa dukkanin waɗanda aka ceto na cikin ƙoshin lafiya.
Haka kuma, ya ce jami’an tsaro sun kama mutane bakwai da ake zargi da hannu a lamarin, yana mai bayyana hakan a matsayin wani gagarumin ci gaba a binciken da ake yi.
Kwamishinan ya ƙara da cewa ana ci gaba da bincike domin gano sauran masu hannu a satar tare da gurfanar da waɗanda aka kama a gaban kuliya.
