News
Makafi 135 Ne Suka Rubuta Jarrabawar JAMB A Kano
A Jihar Kano da ke arewacin Najeriya, aƙalla ɗalibai 135 masu lalurar gani ne suka rubuta Jarrabawar Shiga Manyan Makarantu (UTME) ta shekarar 2026, karkashin shirin da Hukumar JAMB ke gudanarwa domin tallafa wa masu buƙatu na musamman.
Wannan na zuwa ne yayin da shirin ya cika shekaru goma da ƙaddamar da shi a shekarar 2017, da nufin bai wa ɗalibai masu nakasa damar shiga jarrabawar cikin sauƙi da adalci kamar sauran takwarorinsu.
Fashin Offa: Ofishin Mai Shigar Da Ƙara Ya Wanke Saraki Tun 2018
Da yake zantawa da manema labarai, Koodinetan cibiyar Kano, Farfesa Muhammad Yahuza Bello, ya ce adadin ɗaliban da suka rubuta jarrabawar a Kano ya kai sama da kashi 25 cikin ɗari na dukkan ɗalibai masu buƙatu na musamman a faɗin Najeriya.
Ya bayyana cewa cibiyar Kano tana karɓar ɗalibai daga jihohin Kano da ma makwabta irin su Jigawa, Katsina, Kaduna da Zamfara.
A cewarsa, Hukumar JAMB ta samar da muhimman tallafi ga ɗaliban, ciki har da masauki kyauta, abinci da tallafin sufuri domin sauƙaƙa musu halartar jarrabawar.
Farfesa Bello ya kuma ce an maida kuɗin rajista ga waɗanda suka bayyana nakasarsu tun da wuri, tare da ba su damar amfani da kayan taimako kamar taɓe-taɓe, allo da stylus ko kuma masu fassara, ganin cewa ba sa iya amfani da tsarin jarrabawar kwamfuta (CBT) kai tsaye.
A cewarsa, cikin shekaru goma da suka gabata, sama da ɗalibai 5,000 masu buƙatu na musamman ne suka rubuta UTME a ƙarƙashin wannan shiri, inda kusan kashi 34 cikin ɗari daga cikinsu suka samu guraben karatu a manyan makarantu.
Ya ƙara da cewa wannan tsari wata shaida ce ta ƙoƙarin Najeriya wajen tabbatar da ilimi mai haɗa kowa da kowa, yana mai cewa JAMB na zama abin koyi a Afirka.
A bana kuma, ana sa ran sama da ɗalibai 530 masu nakasa daban-daban za su rubuta jarrabawar a cibiyoyi 11 da aka tanada a faɗin ƙasar.
