News
‘Yan Bindiga Sun Hallaka Direban Bas, Sun Yi Awon Gaba Da Fasinjoji A Hanyar Benin Zuwa Lagos
Wasu da ake zargin ‘yan garkuwa da mutane ne sun kashe direban wata motar haya tare da sace fasinjojinta a wani hari da suka kai a babbar hanyar Benin zuwa Lagos a Jihar Edo.
Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne a ranar Lahadi, 19 ga Afrilu, 2026, a kan hanyar Benin zuwq Ore, yayin da motar ke kan hanyarta daga Lagos zuwa yankin Gabashin Najeriya.
An ce maharan sun yi wa motar kwanton ɓauna, inda suka buɗe mata wuta, lamarin da ya tilasta ta tsayawa. Nan take aka harbe direban har lahira, yayin da aka tura sauran fasinjojin cikin daji.
Wani bidiyo da ya bazu a shafukan sada zumunta ya nuna yadda aka bayyana cewa maharan sun tare motar ne suna tafiya zuwa Gabas, inda suka kashe direban tare da kwashe fasinjojin zuwa cikin daji.
Rundunar ‘yan sandan Jihar Edo ta tabbatar da aukuwar lamarin. Jami’ar hulɗa da jama’a ta rundunar, ASP Eno Ikoedem, ta ce tuni aka kaddamar da farautar waɗanda ake zargi.
Ta ƙara da cewa jami’an tsaro sun fara aikin bincike a cikin dazuka domin ceto mutanen da aka sace tare da cafke maharan.
