Connect with us

News

Harin Kasuwar Siyar Da Wayoyi Ta Farm Cente Ya Jefa ’Yan Kasuwa Cikin Fargaba

Published

on

IMG 20260429 WA0002

Harin da wasu da ake zargin ’yan daba masu alaƙa da siyasa suka kai Kasuwar Siyar Da Wayoyi Ta Farm Cente da ke Kano ya janyo hankalin jama’a, inda ake ganin lamarin wata babbar barazana ce ga zaman lafiya da ci gaban tattalin arziki a jihar, musamman yayin da ake tunkarar zaɓen 2027.

‎Lamarin ya faru ne a ranar Litinin, 27 ga Afrilu, 2026, inda aka ga yadda wasu suka mamaye kasuwar, suka yi sace-sace, tare da lalata dukiyoyi ciki har da motoci da babura. Haka kuma, mutane da dama sun samu raunuka a yayin harin.

Advertisement

Allah Ya Yiwa Tsohon Shugaban Hukumar KNUPDA Rasuwa Wato TPL Alhaji Isyaku Mukhtar Kura

‎Kasuwar Farm Centre na daga cikin manyan cibiyoyin kasuwancin wayoyi da fasahar sadarwa a Arewacin Najeriya, wadda ke jan hankalin ’yan kasuwa daga sassa daban-daban na ƙasar har ma da maƙwabta.

Advertisement

‎Saboda haka, duk wata barazana ga kasuwar na da tasiri kai tsaye ga tattalin arzikin Kano.

‎Wannan lamari ya sake jefa ’yan kasuwa cikin damuwa, musamman duba da cewa da yawa daga cikinsu har yanzu ba su gama murmurewa daga gobarar da ta taba aukuwa a kasuwar ba.

Advertisement

‎Har ila yau, kasancewar ofishin fasfo na Kano yana kusa da wurin da lamarin ya faru, ya ƙara nuna yadda batun tsaro ke bukatar kulawa ta musamman, domin irin wannan tashin hankali na iya jawo damuwa ga baƙi da masu zuba jari.

‎Ko da yake wani ɗan siyasa da ake danganta shi da harin ya musanta hannu a ciki, masu sharhi na ganin cewa lamarin ya nuna yadda rikicin siyasa ke ƙara tsananta, musamman idan aka kasa dakile mabiyan ’yan siyasa.

Advertisement

‎’Yan sanda sun yi gaggawar ɗaukar mataki, inda suka yi amfani da hayaki mai sa hawaye domin tarwatsa masu tayar da hankalin, tare da kama mutum shida. Sai dai duk da haka, ana ganin har yanzu akwai gibi a ɓangaren tsaro a irin wannan muhimmiyar kasuwa.

‎Masana sun shawarci gwamnatin Kano da ta ƙara ƙarfafa jami’an tsaro, musamman rundunar ’yan sintiri da Hukumar Tsaron Unguwanni, domin tabbatar da tsaro a muhimman wuraren kasuwanci.

Advertisement
  • Shawarwari

‎Masu ruwa da tsaki sun bayar da wasu shawarwari kamar haka:

‎’Yan siyasa su rungumi zaman lafiya tare da jan kunnen mabiyansu

‎A binciki lamarin tare da hukunta duk wanda aka samu da laifi

Advertisement

‎A ƙara tsaro a Farm Centre ta hanyar haɗin gwiwar jami’an tsaro

‎Gwamnati ta samar da rundunar gaggawa don kare kasuwanni

Advertisement

‎A ƙarfafa wayar da kai kan muhimmancin zaman lafiya a siyasa

‎Masu sharhi na ganin Kano na fuskantar wani muhimmin lokaci, inda dole ne a ɗauki matakan kare zaman lafiya da martabar jihar a matsayin cibiyar kasuwanci a Arewa.

Advertisement

‎Sun jaddada cewa, bai kamata a bar rikicin siyasa ya zama sanadin lalacewar dukiyoyi da rayuka ba, tare da kira ga kowa da kowa da ya mara baya wajen tabbatar da zaman lafiya kafin zaɓen 2027.

 

Advertisement

Comrade Abbas Ibrahim writes from Kano and can be reached @ abbasibrahim664@gmail.com

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending