Entertainment
An Kama Wata ‘Yar TikTok Da Ke Barazana Ga Rayuwar Shugaban Kasa
Jami’an ’yan sandan ƙasar Ghana sun cafke wata matashiya mai suna Mahama Aminat bisa zargin yi wa shugaban ƙasar, John Dramani Mahama, barazana tare da tunzura jama’a su kai masa hari ta hanyar amfani da kafar TikTok.
Rahotanni sun nuna cewa an kama wadda ake kira Akosua Serwaa Minat ne a yankin Ashanti bayan wani samame na haɗin gwiwa da jami’an yaƙi da laifukan yanar gizo da kuma jami’an leken asiri suka gudanar.
A cikin wata sanarwa da rundunar ’yan sandan Ghana ta fitar, ta ce matashiyar ta wallafa wasu bidiyo a TikTok inda ake zargin ta yi kalaman batanci ga shugaban ƙasar tare da barazanar kashe shi da kuma tunzura wasu su kai hari ga shugaban da mai dakinsa.
Sanarwar ta ƙara da cewa sashen Cyber Vetting and Enforcement Team (CVET) ne ya gudanar da bincike kan lamarin bayan bidiyon sun bazu a kafafen sada zumunta, lamarin da ya taimaka wajen gano inda take tare da cafke ta a Sekyere Zongo da ke yankin Ashanti.
’Yan sandan sun tabbatar da cewa a halin yanzu matar tana tsare a hannunsu, yayin da ake sa ran gurfanar da ita a gaban kotu nan ba da jimawa ba.
-
News5 days ago
Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Kai Ziyarar Ba Zata Asibitin Kwararru Na Best Choice Dake Kano
-
News6 days ago
An Tura Kwamishinonin ’Yansanda 30 Da Jami’ai 15,000 Domin Sanya Ido A Zaɓen Osun
-
News3 days ago
El-Rufa’i Ya Shigar Da Ƙarar Neman Diyyar Biliyan N10 Bisa Zargin ICPC Da Nesanta Shi Da Iyalansa
