Connect with us

News

Matashiya Mai Koyon Tuƙi Ta Murƙushe Yara Uku ’Yan Gida Ɗaya

Published

on

Wata matashiya da ke koyon tuƙi ta murƙushe wasu yara uku ’yan gida ɗaya bayan da mota ta kutsa cikin gidansu a yankin Ogbunabali da ke birnin Fatakwal na Jihar Ribas.

Rahotanni sun bayyana cewa hatsarin ya faru ne yayin da wani saurayi ke koyar da budurwarsa tuƙi, inda a wani lokaci ta rasa yadda za ta sarrafa motar, lamarin da ya sa motar ta afka cikin gidan da yaran ke ciki.

Advertisement

An Kama Wata ‘Yar TikTok Da Ke Barazana Ga Rayuwar Shugaban Kasa

Yaran da hatsarin ya rutsa da su na da shekaru 10, 4 da kuma 3, kuma rahotanni sun ce sun mutu nan take sakamakon mummunan hatsarin.

Advertisement

 

Wata majiya daga yankin ta shaida cewa aukuwar lamarin ta tayar da hankali matuƙa a unguwar, yayin da mahaifiyar yaran ta shiga cikin matsanancin alhini tana neman a yi mata adalci.

Advertisement

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ribas ta tabbatar da faruwar lamarin, tana mai cewa an kaddamar da bincike domin gano cikakken musabbabin hatsarin.

Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, Olugbenga Adepoju, ya bayyana jimaminsa kan lamarin, inda ya tabbatar da cewa za a bi diddigin lamarin dalla-dalla tare da hukunta duk wanda bincike ya nuna yana da hannu a aukuwar hatsarin.

Advertisement

Har ila yau, rundunar ta bukaci jama’a da su kwantar da hankalinsu tare da bai wa jami’an tsaro cikakken haɗin kai yayin gudanar da bincike.

 

Advertisement

 

Aminiya

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending