Labarai
El-Rufa’i Zai Rabawa Talakawan Kaduna Tallafin Biliyan N4b Don Rage Radadin Talauci

Daga muslim yunus abdullahi
Gwamnatin jihar Kaduna ta ware Naira Biliyan hudu da zata rarrabawa talakawa a duka kananan hukumomi 23 dake fadin jihar a shirinta na tallafawa mararsa karfi domin su dogara da kansu.
Bayanin hakan ya fito ne daga Kwamishinan kasafi da tsare-tsare na jihar Muhammad Sani Abdullahi (Dattijo), a yayin ganawarsa da yan Jaridar a Ofishinsa.
Kwamishinan yace shirin tallafin zai bawa Gwamnati damar jin kan jama’a kai tsaye musamman mazauna karkara.
– Advertisement –
Muryoyi ta ruwaito Dattijo yace Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai nada azamar ganin jama’a sun samu rayuwa cikin wadata da walwala shi yasa ya kagu wajen ganin an ninka kudaden tallafin ya haura Biliyan N24 a shekara mai zuwa.
Za a rabar da kudaden ne a karkashin shirin rage radadin talauci da Gwamnatin jihar Kaduna ta kirkiro kuma zata kaddamar a sabuwar shekara
-
Labarai6 days ago
Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Yi Wa Masu Digirin Ƙasashen Waje Jarrabawa
-
Labarai2 days ago
Jami’an Tsaro A Pakistan Sun Kama ’Yan Najeriya 20 Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi
-
Labarai1 day ago
Hare-haren Ta’addanci Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutum 835 A Najeriya Cikin Wata Guda – Rahoto
