Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, ya ce kusan kashi biyu cikin uku na yaran Ukraine sun tsere daga gidajensu cikin makwanni shida da mamayar da Rasha ta yi wa kasar.
Majalisar Dinkin Duniya ta kuma tabbatar da mutuwar yara 142, duk da cewa ta yi gargadin adadin ka iya fin haka.
Daraktan shirin gaggawa na UNICEF Manuel Fontaine, wanda ya dawo daga ziyarar aiki Ukraine, ya ce farar-hula kusan miliyan biyar ne suka rasa muhallansu, yayin da yara sama da miliyan bakwai suka shiga gararamba cikin kankanen lokaci, lamari ne da bai taba ganin ya faru cikin sauri ba a shekaru 31 da ya kwashe yana aikin jinkai.
Fonteine ya shaida wa Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya cewa ” cikin yara kanana miliyan uku da dubu 200 da suka rage a gidajensu, kusan rabinsu na cikin hadarin rasa isasshen abinci.”
Ya yi gargadin lamarin zai munanan a birane kamar Matiupol da Kherson, inda babu ruwa mai tsafta, babu abinci, sannan babu magani.
A bangare guda kuma, jakadan Ukraine a Majalisar Dinkin Duniya, Sergiy Kyslytsya, ya yi ikirarin Rasha ta dauke yaran kasar sama da 121,000, sun kuma fara shirin ba da rikonsu ga iyalai Rashawa.
Sai dai Fontaine ya ce kawo yanzu babu shaidar da za ta tabbatar da wannan ikirari, amma UNICEF za ta gudanar da bincike domin gano gaskiyar ikirarin nasa.
