Connect with us

News

An yanke wa wani mutum ɗaurin shekaru 7 a gidan yari sakamakon barazanar kashe Firaministan Spain

Published

on

Daga yasir sani abdullahi

 

 

Kotun Spain ta yanke wa wani mutum hukuncin ɗaurin shekaru bakwai a gidan yari bisa samunsa da laifin yin barazanar kashe Firaministan Spain, Pedro Sanchez.

Manuel Murillo, mai shekaru 66, ya wallafa sakonni a shafukansa na sada zumunta da kalaman barazana ga Sanchez.

Ƴan sanda sun kai sumame gidan Murillo kuma sun kama haramtattun makamai guda bakwai, ciki har da bindiga mai sarrafa kanta.

Advertisement

Kotun ta yanke hukuncin cewa Murillo ya yanke cewa mutuwar Firaministan ita ce kaɗai mafita don kawo sauyi a siyasar Spain.

Alkalan sun kuma ce makaman da aka kama a wajen Murillo na nuni da cewa akwai hatsarin gaske.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending