Connect with us

News

Gwamnatin Tarrayya Ta Musanta Zargin Ɓoye Kusan Triliyan 9 Don Yaƙin Neman Zaɓen Baɗi

Published

on

Tinubu

Gwamnatin Tarayya ta yi watsi da zargin da ke cewa ta ɓoye kusan Naira Tiriliyan 8 daga kasafin kuɗin shekarar da ta gabata domin amfani da su wajen shirye-shiryen zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.

Martanin gwamnatin ya biyo bayan zargin da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi na cewa akwai kuɗaɗe da yawansu ya kai Naira Tiriliyan 8 da wasu biliyoyin naira da ba a bayyana yadda aka kashe su ba, yana mai zargin cewa an ajiye su ne domin yaƙin neman zaɓe mai zuwa.

“Ku Yi Aiki Ko Ku Sauka” — Gwamnan Kano Ya Gargaɗi Masu Riƙe Da Muƙaman Gwamnati

Atiku ya ce zargin nasa ya samo asali ne daga rahoton Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF), wanda ya yi nuni da cewa akwai gibin kuɗaɗe da ya kai kusan kashi biyu cikin ɗari na tattalin arzikin Najeriya da har yanzu ba a yi cikakken bayani a kansa ba.

Sai dai Gwamnatin Tarayya ta ce zargin bai da tushe, tana mai jaddada cewa babu wata hujja daga IMF ko wani ɓangare da ta tabbatar da cewa an ɓoye kuɗaɗen ko an karkatar da su domin wata manufa ta siyasa.

 

Advertisement

Rahoton IMF ya haifar da ce-ce-ku-ce a faɗin ƙasar, inda jam’iyyun adawa da ƙungiyoyin fararen hula suka bukaci gwamnati ta fito ta yi cikakken bayani kan yadda aka tafiyar da kuɗaɗen.

 

A nasa ɓangaren, Atiku ya buƙaci hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa, musamman EFCC da ICPC, su gudanar da bincike kan lamarin, yayin da Peter Obi ya buƙaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi wa ‘yan Najeriya bayani kan zarge-zargen.

A cikin sanarwar da gwamnatin ta fitar mai ɗauke da sa hannun Ministan Kuɗi, Taiwo Oyedele, ta bayyana cewa zarge-zargen ba su da ingantacciyar hujja, tana mai cewa babu wata shaida da ke nuna cewa an ɓoye kuɗaɗen kamar yadda ake ikirari.

Sai dai sanarwar ba ta fayyace inda kuɗaɗen da ake magana a kansu suke ko yadda aka sarrafa su ba, lamarin da ya ci gaba da janyo muhawara a tsakanin masu ruwa da tsaki.

 

Advertisement

 

RFI

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending