Connect with us

News

Singapore Za Ta Tallafawa Yaran Kasar Da Miliyan 90

Published

on

singapore dollar (1)

Gwamnatin Singapore ta sanar da sabon tsarin tallafa wa iyalai, wanda zai sa kowane yaro ɗan ƙasar da ya cancanta ya samu tallafin gwamnati da ya kai kusan S$70,000, kwatankwacin Naira miliyan 94, daga haihuwa har zuwa shekara 17.

Firaministan ƙasar, Lawrence Wong, ya bayyana hakan ne a jawabinsa na National Day Rally da ya gabatar a ranar Lahadi, 23 ga Agusta, 2026.

Mutane 30 sun mutu A Bayan Zaftarewar Ƙasa A Wurin Zubar Da Shara

Sabon shirin mai suna SG Child Support Package ya ƙunshi tallafi daban-daban da gwamnati za ta rika bai wa iyalai domin rage musu nauyin kula da ’ya’yansu.

A ƙarƙashin shirin, za a bai wa kowane yaro S$10,000 a matsayin tallafin haihuwa, yayin da S$32,000 za a bayar a matsayin Child Credits.

Haka kuma, gwamnati za ta ware S$5,000 a matsayin tallafin Child Development Account (CDA), tare da ƙarin tallafin gwamnati da zai kai S$5,000.

Advertisement

Bugu da ƙari, za a ƙara S$10,000 a asusun karatun yaro idan ya kai shekara 17.

Gwamnatin ta ce idan aka haɗa waɗannan tallafe-tallafen da sauran shirye-shiryen da ake da su, ciki har da S$5,000 na MediSave Grant for Newborns da kuma tallafin Edusave na shekara-shekara, jimillar tallafin da kowane yaro zai samu za ta kai kusan S$70,000.

Wannan ya haura tallafin da iyaye ke samu a yanzu, wanda yake tsakanin S$27,500 zuwa S$56,500, gwargwadon yawan ’ya’yan da suke da su.

Da yake jawabi kan shirin, Wong ya ce gwamnati na son sauƙaƙa tsarin tallafin iyalai tare da tabbatar da cewa kowane yaro zai samu tallafi cikin adalci.

Ya ce gwamnati ba za ta mayar da hankali kan tallafin lokacin haihuwa kaɗai ba, sai dai ta ci gaba da tallafa wa iyalai yayin da yara ke girma.

Ana sa ran sabon tsarin zai amfani sama da yara 610,000 daga gidaje kusan 380,000.

Advertisement

A cewar gwamnatin, S$10,000 na tallafin haihuwa za a biya shi kashi biyu cikin shekarar farko bayan haihuwar yaro, yayin da za a rika bayar da S$2,000 a duk shekara daga lokacin da yaro ya cika shekara ɗaya har zuwa shekara 16.

Haka kuma, lokacin da yaro ya kai shekara 17, za a ƙara masa S$10,000 a asusun karatunsa na gaba da sakandare.

Matakin na daga cikin ƙoƙarin Singapore na ƙarfafa haihuwar ’ya’ya, yayin da ƙasar ke fuskantar raguwar yawan haihuwa.

Firaminista Wong ya ce tallafa wa iyalai da ’yan ƙasar na daga cikin manyan abubuwan da gwamnatin ƙasar ta sanya a gaba.

Sai dai, ba wai za a bai wa ma’aurata Naira miliyan 94 a tsabar kuɗi lokaci guda ba. Adadin ya ƙunshi jimillar fa’idodin tallafin gwamnati da kowane yaro zai samu daga haihuwa har zuwa shekara 17.

 

Advertisement

 

VANGUARD

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending