Connect with us

News

Jami’an ’Yan Sanda Sun Ceto Mutane Uku Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Makarfi

Published

on

1787579968700

Jami’an tsaro a Jihar Kaduna sun yi nasarar ceto mutane uku da aka yi garkuwa da su, bayan kai samame wata maboyar da ake zargin ’yan bindiga ne suka kafa a ƙaramar hukumar Makarfi.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ta ce an gudanar da samamen ne a ranar Alhamis, bayan da jami’an tsaro suka samu sahihan bayanan sirri kan motsin wasu mutane da ake zargi da aikata laifuka a yankunan Gidan Mijin Gwaggo da Durum.

Pantami Da Yaransa Sun Fantama Min Ƙarya, Domin Babu Inda Na Ba Shi Haƙuri, Inji Hajiya Naja’atu Muhammad

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, Mansir Hassan, ya bayyana cewa kwamishinan ’yan sandan jihar, Rabiu Muhammad, ne ya bayar da umarnin jami’an rundunar Makarfi, tare da ’yan banga, su kai samame wuraren da ake zargin ’yan bindigar ke fakewa.

A cewarsa, da jami’an tsaron suka isa yankin, waɗanda ake zargin ’yan bindiga ne sun buɗe musu wuta, lamarin da ya haifar da musayar wuta mai tsanani tsakanin ɓangarorin biyu.

Rundunar ta ce sakamakon matsin lambar da jami’an tsaron suka yi, ’yan bindigar sun tsere zuwa cikin daji, yayin da ake zargin wasu daga cikinsu sun samu raunuka sakamakon harbin bindiga.

Advertisement

Bayan fatattakar ’yan bindigar, jami’an tsaron sun binciki wani gida mallakin wani mutum mai suna Yakubu Sule, inda suka gano cewa ana amfani da gidan a matsayin maboyar masu garkuwa da mutane.

A yayin binciken, jami’an sun gano mutane uku da aka yi garkuwa da su, ciki har da Alhaji Hamza Gimi, inda aka samu nasarar kubutar da su ba tare da sun samu wani rauni ba.

Rundunar ta ce an miƙa waɗanda aka ceto ga iyalansu bayan tabbatar da lafiyarsu.

Haka kuma, jami’an tsaron sun kwato wani babur kirar Boxer, wanda ake zargin masu garkuwa da mutanen sun yi amfani da shi wajen gudanar da ayyukansu.

Rundunar ’Yan Sandan ta ce tana ci gaba da gudanar da bincike da farautar waɗanda suka tsere, domin tabbatar da an gurfanar da su a gaban ƙuliya domin fuskantar hukunci bisa doka.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending