Connect with us

News

LAUYOYI SUN KOKA DA SAKIN SAKIN DARIYE DA NYAME DA SHUGABA BUHARI YA YI

Published

on

Daga mujahid danlami garba

 

 

Lauyoyi da masu bincike da jami’an tsaron da su ka tabbatar da ganin an hukunta gwamnoni biyu da aka yi wa afuwa, sun ce Shugaba Buhari ya watsa masu kasa a ido.

Hukumar EFCC dai ta kashe miliyoyin kudi wajen gurfanar da da Jolly Nyame da Joshua Dariye kamar yadda Lauyoyi sun bayyana.

Jami’an hukumar EFCC da su ka hukunta gwamnonin sun ce ba kananan kudade aka kashe tsakanin shekara ta 2007 da 2018 ba,
musamman Joshua Dariyae, wanda sai da aka rika kawo shaida daga London, kuma ana biyan kudin kawo shi.

Advertisement

Wani jami’in EFCC da ya bukaci a sakaya sunan sa, ya ce sai da mabiya Dariye fasa kan daya daga cikin ‘yan sandan da ke binciken sa mai suna Ilyasu Kwarbai da marikin bindiga a Jos.

Wata majiya ta ce, Lauyan da EFCC ta dauka wajen gurfanar da tsofaffin gwamnonin Rotimi Jacobs, ya bayyana bacin ran sa a kan abin da shugaba Buhari ya yi.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending