Connect with us

News

Jami’an Ƴansanda Sun Kama Ba’indiye Da Jami’an Tsaro Biyu Kan Zargin Cin Zarafin Direbobi  ‎

Published

on

IMG 20261014 002427 610

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Oyo ta kama wani ɗan ƙasar Indiya, Harjit Singh, mai shekaru 46, da jami’an tsaro biyu bisa zargin cin zarafin direbobin manyan motoci biyu a wani kamfani da ke Ibadan.

Kamen ya biyo bayan yaɗuwar wani faifan bidiyo da ya nuna lamarin a kamfanin Karma Agric Feeds and Foods Limited, da ke kan hanyar Legas zuwa Ibadan.

Jami’an Ƴansanda Sun Kama Ba’indiye Da Jami’an Tsaro Biyu Kan Zargin Cin Zarafin Direbobi  ‎

Kakakin rundunar, DSP Ayanlade Olayinka, ya ce rikicin ya samo asali ne daga saɓani kan wurin ajiye mota, bayan da tayar motar ta fashe, sannan kamfanin ya ƙi sauya ta.

An bayyana direbobin da abin ya shafa a matsayin Ridwan Olajide, mai shekaru 34, da Taiwo Yinusa, mai shekaru 37. An kai su asibiti domin samun kulawar likitoci.

Rundunar ta ce an miƙa lamarin ga Sashen Bincike na Musamman da ke Eleyele, Ibadan, domin ci gaba da bincike da tantance waɗanda ke da alhakin abin da ya faru.

Advertisement

 

PUNCH

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending