News
Jami’an NDLEA Sun Kama Sama Da Mutum 100 Kan Zargin Ta’ammali Da Miyagun Kwayoyi A Kaduna
Hukumar Hana Sha da Safarar Muggan Kwayoyi ta Kasa NDLEA reshen jihar Kaduna ta kama mutum 108 da take zargin su da laifin safarar muggan kwayoyi sannan ta kwato tan 1,897.907 na muggan kwayoyi a watan Satumba a jihar.
A dalilin ayyukan hukumar kotu ta gurfanar da mutum 12 daga cikin yawan mutanen da hukumar ta kama da laifin safarar muggan kwayoyi sannan ta ragargazza mashayar kwayoyi 40 duk a cikin wannan wata.
Jami’in yada labarai na hukumar Sani Garba ya sanar da haka a wani takarda da ya fitar ranar Litini a garin Kaduna.
Jami’an Ƴansanda Sun Kama Ba’indiye Da Jami’an Tsaro Biyu Kan Zargin Cin Zarafin Direbobi
Garba ya ce jami’an hukumar sun kwato muggan kwayoyi da suka hada da ganyen wiwi, tramadol, hodar ibilis, crystal methamphetamine da dai sauran muggan kwayoyi.
Ya ce daga cikin muggan kwayoyin da hukumar ta kwato ganyen wiwi ce ta fi yawa inda ta kai nauyin kilo 1,874.843.
Saura kuwa sun hada da Tramadol kilo 20.749, hodar ibilis 0.007kg, crystal methamphetamine 0.038kg da wasu muggan kwayoyin da nauyin su ya kai 2.269kg.
Garba ya ce Hukumar ta yi wannan kame ne yayin da take gudanar da ayyukanta na yaki da safarar da shan muggan kwayoyi a fadin jihar.
Ya ce Hukumar ta yi kokari wajen hana kafafen safarar muggan kwayoyin da ake da su a jihar ta hanyar ragargazza mashayar muggan kwayoyi 40 a jihar.
Garba ya ce kotu ta yanke wa masu safarar muggan kwayoyi 12 hukunci sannan akwai wasu guda 10 da suke kira a yanke musu hukunci.
Ya ce Hukumar ta ci gaba da gudanar da bincike tare da farautar masu safarar muggan kwayoyi a jihar.
Garba ya ce NDLEA ta dauki wasu matakai da suka hada da wayar da kan mutane illar dake tattare da sha ko safarar muggan kwayoyi tare da samar da kula wa wadanda ke fama da matsalolin da ake samu a dalilin ta’amali da muggan kwayoyi domin ganin an rage safarar da bukatan muggan kwayoyi a jihar.
Shugaban Hukumar Maijama’a Muhammad ya yaba da namijin kokarin da jami’an hukumar ke yi wajen yaki da sha da safarar muggan kwayoyi a jihar.
Ya kuma yaba da goyan bayan da hukumar ke samu daga wajenasu ruwa da tsaki a jihar inda yake cewa a dalilin goyan bayan su ne hukumar take samun nasarori irin haka.
Garba ya yi kira ga mutane da su ci gaba da hada hannu da Hukumar domin ganin an yaki sha da safarar muggan kwayoyi a jihar Kaduna.
-
News13 hours ago
Kwararren Mai Daukar Hoton Labari Maikatanga Ya Shiga Sahun Kwamitin Alkalan Gasar Wole Soyinka Ta 2026
-
News5 days ago
Cutar Mashaƙo Ta Yi Ajalin Yara Biyar ‘Yan Gida Daya Cikin Mako Guda A Kano
-
News7 days ago
Allah Ya Yi Wa Kakakin Hukumar Kashe Gobara Ta Jihar Kano, CFO Saminu Yusuf Abdullahi, Rasuwa
