Labarai
An Daure Sama Da Mutum 200 Kan Hakar Zinare Ba Bisa Ka’ida Ba

Wata kotu a ƙasar Guinea ta yanke wa mutane 202 hukuncin ɗaurin shekaru uku a gidan yari bisa samunsu da laifin haƙar zinare ba bisa ƙa’ida ba a yankin Siguiri da ke arewa maso gabashin ƙasar.
Hukuncin na zuwa ne a wani mataki na ƙara tsaurara matakan dakile haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba, musamman a yankin da ke kusa da iyakar ƙasar Mali.
Dakarun Soji Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Safarar Harsasai 300 A Kogi
Baya ga haka, kotun ta yanke wa tsofaffin jami’an gwamnati 22 na yankin hukuncin ɗaurin shekaru biyu bayan samunsu da laifin taimakawa wajen lalata muhalli da kuma gurɓata hanyoyin ruwa.
Rahotanni sun nuna cewa wasu daga cikin mutanen da aka daure bisa haƙar zinaren ba bisa ƙa’ida ba ‘yan ƙasashen waje ne.
Sai dai matakin da hukumomin ƙasar suka ɗauka ya haifar da zanga-zanga da tashin hankali, inda arangamar da ta barke tsakanin masu zanga-zangar da jami’an tsaro a makon da ya gabata ta yi sanadin mutuwar mutane 10, yayin da wasu 13 suka jikkata.
A wani rahoto da Shirin Kare Muhalli na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNEP) ya fitar, an bayyana cewa haƙar zinare ba bisa ƙa’ida ba na samar wa fiye da mutane 300,000 hanyoyin samun abin dogaro da kai.
Sai dai hukumomin Guinea na ƙoƙarin dakile wannan sana’a saboda illolin da take haifarwa ga muhalli, musamman gurɓata ruwa da lalata muhallin al’umma.
