News
2023: ” ‘Yan Nijeriya Ne Kadai Ke Da Alhakin Zabo Magajin Kujera Ta Ba Ni Ba” -Buhari
Daga Suleiman ado ahmad
A daidai lokacin da kakar babban zaben shekarar 2023 a Nijeriya ke kara karato wa, Shugaba Muhammadu Buhari ya sake yin magana kan magajin buzun Karagarsa.
A kwankin baya cikin wani shirin talabijin an jiyo shugaba Buharin na furata cewa, ya na wanda yake son ya dare Karagarsa, amma bai kai ga bayyana sunan wanda zai gaje shinba don gudun kar a farwa wanda zai gaje shin.
Buhari, ya sake maimaita maganar a jiya Litinin bayan an sauko daga Sallar Idin karamar sallah ta bana da aka gudanar a Barikin Mambilla da ke Abuja, inda ya kara jaddada kudurinsa na ganin an gudanar da tsaftatancen zabe a 2023.
Shugaban ya kuma umarci shugabannin rundunar tsaron soji da sauran jami’an tsaro da su yi dukkan mai yuwa don don fatattakar ‘yan ta’adda da kuma kawo karshensu.
“Aikinsu ne su gano malafar ‘yan ta’adda tare da kawo karshensu, zamu ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin daukcin ‘yan Nijeriya, musamman saboda manoma su koma gona su ci gaba da noma don a wadata kasa da abinci “. In ji Shugaba Buhari
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
