Labarai
Bayan kammala ‘Next Level’, babban lauya ya nemi a kara wa Buhari wa’adin mulki

Babban Lauya, kuma dattijon kasa, Cif Robert Clarke (SAN), ya yi kira da a kara wa shugaban kasa Muhammadu Buhari wa’adin mulki bayan kammala mulkinsa na biyu a 2023, Daily Trust ta ruwaito.
Babban lauyan, wanda ya bayyana hakan a ranar Litinin din da ta gabata, ya bayyana cewa watannin da ke gabanin zaben 2023 ba su isa su kawo karshen rashin tsaro ba, balle a iya zabe cikin kwanciyar hankali.
Da yake magana a gidan talabijin na Arise, Clarke ya ci gaba da cewa kundin tsarin mulkin kasar ya tanadi cewa shugaban kasa zai iya tsawaita wa’adinsa na tsawon watanni shida, tun da farko, idan yana jin cewa gudanar da zabe zai iya zuwa da tasgaro.
Ya ce ba daidai ba ne a yi imani cewa Shugaban kasa ba zai iya ci gaba da zama a karagar mulki sama da shekaru takwas na wa’adin mulki biyu ba. Clarke ya ce shugaban kasar na iya kara wa kansa wa’adin watanni shida domin gudanar da zabe cikin lumana.
-
Labarai7 days ago
Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Yi Wa Masu Digirin Ƙasashen Waje Jarrabawa
-
Labarai3 days ago
Jami’an Tsaro A Pakistan Sun Kama ’Yan Najeriya 20 Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi
-
Labarai2 days ago
Hare-haren Ta’addanci Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutum 835 A Najeriya Cikin Wata Guda – Rahoto
