Connect with us

News

An daure wani attajiri a kan zargin cin zarafin marayu

Published

on

Daga kabiru basiru fulatan 

 

Wata kotu a kasar Masar ta yanke wa mamallakin kafafen watsa labarai, kuma makusancin gwamnati, daurin shekara uku, sakamakon samun shi da hannu a badakalar safarar mutane, da cin zarafin wata yarinya karama a gidan marayun da yake kula da shi.

2023: Muna addu’ar Allah Ya baka nasara, Sarkin Damaturu ya faɗawa Osinbajo

A farkon shekarar nan ne aka cafke Mohamed El-Amin, bayan zarge-zargen cin zarafin yara mata da ke gidan marayun Missing Children, ta hanyar lalata da su.

Mai shigar da kara na gwamnati, ya ce El-Amin ya yi amfani da karfinshi fiye da kima da ganin yaran ba su da galihu wajen cin zarafin nasu.

El-Amin ya musanta aikata laifin, yana kuma da damar daukaka kara kan hukuncin.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending