Connect with us

News

Kola Abiola ya zama dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PRP

Published

on

Daga yasir sani Abdullah 

 

 

 

 

 

Advertisement

Jam’iyyar PRP ta sanar da ɗan takararta na shugaban ƙasa wanda zai fafata a babban zaɓen 2023 da ke tafe, Latef Kola Abiola, shi ne wanda ta bayyana ya lashe tikitin kujera lamba ɗaya na PRP bayan lallasa abokan takara da gagarumin rinjaye, kamar yadda jaridar Legit ta rawaito.

Shugaban jam’iyyar PRP na kasa, Falalu Bello, ya sanar da samun gagarumar nasarar Abiola da kuri’u 2,097 inda ya lallasa babban abokin hamayyasa Alhaji Usman Bugaje, wanda ya samu kuri’u 813.

Ragowar yan takarar sun hada da Patience Ndidi, wacce ta samu kuri’u 329, yayin da Gboluga Mosugu ya biye musu baya da kuri’u 263, bayan kammala kirga kuri’u da Daliget suka kada a jihohi, kuma aka turo zuwa babbar hedikwatar jam’iyyar dake Abuja a jiya Lahadi.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending