News
Korona: An dawo da bada tazara a sahun Sallah a Masallatan Haramin Maka da na Madina
An dawo da dokar tilasta bayar da tazara da sa ka takunkumi a Masallacin Ka’aba a Maka da kuma na Annabi a Madina.
Hukumomin da ke kula da Masallatan Biyu Masu Daraja na Saudiyya ne su ka sanar da hakan.
Matakin zai fara aiki ne daga yau Alhamis, inda hukumomin su ka ce yanzu saka takunkumi da bayar da tazara ya zama wajibi a Masallatan biyu masu tsarki.
Hukumomin sun ce matakin ya shafi masu aikin Umrah da masu ɗawafi da sauran masu Ibada a masallatan biyu.
Sannan an yi gargaɗi ga baƙi da ma’aikatan Masallatan biyu su mutunta dokar.
Dokokin za su riƙa aiki a cikin gidaje da kuma waje inda mutane ke mu’amalar yau da kullum.
A ‘yan kwanakin nan masu kamuwa da korona na ƙaruwa a Saudiyya, lamarin da ya sanya a ka dawo da dokokin kariya da ga kamuwa da cutar, ƙasa da wata biyu da janye dokokin a masallatan biyu.