jihar Borno a Arewacin Najeriya ta ce gidajen ɗaiɗaikun mutane fiye da dubu 956 ne aka rasa a tsawon shekarun da aka yi na rikicin Boko Haram. Adadin ya yi daidai da kimanin kashi ɗaya cikin uku na ɗaukacin gidajen da ke faɗin jihar, Tsawon shekara 12 kenan a na dauki-ba-dadi tsakanin dakarun Najeriya da kungiyar Boko Haram a wasu jihohin Arewa maso Gabashin Najeriyar, da suka hada da Borno da Yobe da kuma Adamawa.
Kuma a tsawon wannan lokaci an rasa rayuka da dukiya mai dimbin yawa, sannan miliyoyi sun rasa matsugunansu.
A cikin sanarwar da mai magana da yawun gwamnatin ta jihar Borno Isa Gusau ya fitar, ya kuma ce an yi asarar gine-gine sama da 660 mallakar hukumomi daban-daban, sanadin wannan rikici na ‘yan ta-da-ƙayar-baya.
BBC ta fahimci cewa gine-ginen da aka rasa mafiya yawa ofisoshin hukumomi ne da suka hada da gidajen yari, da ofisoshin ‘yan sanda da kuma makarantu.
Isa Gusau ya kara da cewa duka bayanan da suka samu wani ɓangare ne na rahoton kimanta ayyukan wanzar da zaman lafiya da farfaɗowa na Bankin Duniya kan yankin Arewa maso Gabas